10 Agusta 2026 - 23:30
Source: ABNA24
An Lalata Matsugunan 'Yan Ta'adda Da’ish 8 A Kirkuk, Iraki

Sojojin Iraki sun sanar da lalata matsugunan 'yan ta'adda na ƙungiyar Da’ish 8 a hare-haren jiragen sama a lardin Kirkuk.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Cibiyar yaɗa labarai ta tsaro da ke da alaƙa da ofishin babban kwamandan sojojin Iraki a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa an gudanar da wannan aiki a cikin tsarin bin diddigin ragowar ta'addanci bisa ingantattun bayanan tsaro da aka tabbatar.

Cibiyar yaɗa labarai ta tsaro ta ci gaba da cewa, bisa ga bayanan da hukumar leƙen asiri ta soji ta ƙasar ta samu, 'yan ta'adda na ƙungiyar Da’ish sun ɓoye a cikin yankin da ke ƙarƙashin kulawar runduna ta 11 na kwamandancin ayyukan Kirkuk.

Dangane da wannan sanarwa, an gudanar da aikin ne tare da tuntubar kwamandan sojin sama, kuma tare da bin diddiga da kulawar kwamitin manufofi a ofishin babban kwamandan sojojin Iraki.

Sanarwar cibiyar yaɗa labarai ta tsaro ta kara da cewa, jiragen yaki sun fara da gano wuraren 'yan ta'adda, sannan suka kai "hare-haren jiragen sama da yawa" bisa anfani dajiragen nau’in "Cessna Caravan," wanda ya yi sanadin cikakken lalata matsugunan wannan ƙungiyar ta'addanci 8.

Wannan kwamitin ya nanata cewa za su bayyana ƙarin cikakkun bayanai daga baya.

..................

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha